17 Amma ya ƙone naman bijimin da fatarsa da tarosonsa a bayan zangon kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
18 Sa'an nan ya kawo rago na yin hadaya ta ƙonawa. Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.
19 Sai ya yanka ragon, ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.
20 Da aka yanyanka ragon gunduwa gunduwa, sai Musa ya ƙone kan, da gunduwoyin, da kitsen.
21 Sa'ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
22 Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.
23 Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.