2 “Ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti.
3 Ka kuma tattara jama'a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.”
4 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama'ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada.
5 Musa ya faɗa wa taron jama'ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
6 Sai Musa ya fito da Haruna da 'ya'yansa maza, ya yi musu wanka.
7 Ya sa wa Haruna zilaika, ya ɗaura masa ɗamara, ya sa masa taguwa, ya kuma sa masa falmaran, ya ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.
8 Ya maƙala masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ya sa Urim da Tummin, a kan ƙyallen.