1 A kan rana ta takwas, Musa ya kirawo Haruna, da 'ya'yansa maza, da dattawan Isra'ila.
2 Sai ya ce wa Haruna, “Kawo ɗan maraƙi marar lahani na yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ka miƙa su ga Ubangiji.
3 Ka faɗa wa Isra'ilawa su ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa,
4 da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.”
5 Sai suka kawo abin da Musa ya umarce su a gaban alfarwa ta sujada. Dukan taron jama'a suka matso kusa, suka tsaya a gaban Ubangiji.