2 Zuciyar mai hikima takan kai shi ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan kai shi ga yin mugun abu.
3 Ko lokacin da wawa yake tafiya a hanya, yakan nuna ba shi da hankali, yakan kuma bayyana wa kowa shi wawa ne.
4 Idan mai mulki ya husata da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.
5 Akwai mugunta wadda na gani a duniya, wato kuskuren da masu mulki suke yi.
6 Ana ba wawaye manyan matsayi, attajirai kuwa ana ƙasƙantar da su.
7 Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, shugabanni kuwa suna tafiya a ƙasa kamar bayi.
8 Wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki. Wanda kuma ya rushe katanga, shi maciji zai sara.