6 Ana ba wawaye manyan matsayi, attajirai kuwa ana ƙasƙantar da su.
7 Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, shugabanni kuwa suna tafiya a ƙasa kamar bayi.
8 Wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki. Wanda kuma ya rushe katanga, shi maciji zai sara.
9 Wanda yake farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni. Wanda kuma yake faskare itace yana cikin hatsarinsu.
10 Idan gatari ya dakushe ba a wasa shi ba, dole ne a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma hikima takan taimake shi ya ci nasara.
11 Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani.
12 Maganar mai hikima alheri ce, amma maganganun wawa za su hallaka shi.