1 Ka jefa kyautarka a baya, ka tsince ta a gaba.
2 Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.
3 Idan gizagizai sun cika da ruwa sukan sheƙar da shi ƙasa. A inda itace ya faɗi, a nan zai kwanta, ko wajen kudu ko arewa.
4 Wanda yake la'akari da iska, ba zai yi shuka ba, wanda kuma yake la'akari da gizagizai, ba zai yi girbi ba.