12 Mutum biyu za su iya kāre kansu su ci nasara, amma mutum ɗaya ba zai iya kāre kansa ya ci nasara a kan wanda ya kawo masa hari ba. Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa.
13-14 Mutum yana iya tashi daga matsayin talauci ya zama sarki a ƙasarsa, ko ya fita daga kurkuku ya hau gadon sarauta. Amma lokacin da sarki ya tsufa, idan wautarsa ta hana shi karɓar shawara, bai fi saurayin ɗin da yake talaka mai basira ba.
15 Na yi tunani a kan dukan mutanen da suke zaune a duniyan nan, sai na gane a cikinsu akwai saurayin da zai maye matsayin sarkin.
16 Mutanen da sarki yake mallaka suna da yawan gaske. Amma bayan ba shi ba wanda zai gode masa saboda ayyukan da ya yi. Hakika wannan ma aikin banza ne, harbin iska kawai.