7 Dukan wahalar da ɗan adam yake yi ta samun abinci ce, amma duk da haka bai taɓa ƙoshi ba.
8 Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce kuma matalaucin da ya iya zama da mutane zai samu?
9 Abin da ya zo hannu ya fi dogon buri gama dogon buri aikin banza ne, harbin iska kawai.
10 Kowane abu da ya kasance, an riga an ba shi suna, yadda aka yi mutum haka zai zama. Ba kuwa zai iya gardama da abin da ya fi ƙarfinsa ba.
11 Yawan magana yakan ɓata al'amari. Wane amfani zai yi wa mutum?
12 Wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a 'yan kwanakinsa marasa amfani? Sukan wuce kamar inuwa. Wa kuma zai iya faɗa wa mutum abin da zai faru a duniya bayan rasuwarsa?