1 Kyakkyawan suna ya fi man ƙanshi tsada, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haihuwa.
2 Gara a tafi gidan da ake makokiDa a tafi gidan da ake biki,Gama wannan shi ne ƙarshen dukan mutane.Ya kamata duk mai rai ya riƙe wannan a zuciyarsa,Mutuwa tana jiran kowa.
3 Baƙin ciki ya fi dariya,Gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
4 Mai hikima yakan yi tunanin mutuwa,Amma wawa yakan yi tunanin shagalin duniya.
5 Gara mutum ya ji tsautawar mai hikima,Da ya ji wawaye suna yabonsa.
6 Dariyar wawa kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya ce.Wannan ma aikin banza ne.
7 Hakika zalunci yakan sa mai hikima ya zama wawa,Karɓar rashawa kuma yakan lalata hali.