1 Mutum mai hikima ne kaɗai ya san ainihin ma'anar yadda abubuwa suke. Hikima takan sa shi fara'a, da sakin fuska.
2 Ka kiyaye umarnin sarki saboda alkawarin da ka ɗauka.
3 Sarki yana iya yin kowane abu da ya ga dama, don haka ka guje wa wurin da yake, kada ka zauna a wuri mai hatsari haka.
4 Da iko sarki yake aiki, don haka ba mai iya ce masa, “Don me?”
5 Muddin ka kiyaye umarnin sarki gidanka lafiya, mai hikima yakan yi abu, ya kuma san lokacin yi da hanyar da ta dace da yinsa.
6 Akwai lokacin da ya dace, da hanyar da ta dace na yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.
7 Ko ɗaya daga cikinmu ba wanda ya san abin da zai faru, wane ne zai faɗa mana?