1 Ƙaƙa zinariya ta zama duhu!Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke!Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zubeA kowane magamin titi.
2 Darajar samarin SihiyonaTa kai tamanin zinariya tsantsa.To, ƙaƙa ake lissafinsu kamar tukwanen ƙasa,Aikin hannun maginin tukwane?
3 Ko diloli ma sukan ba 'ya'yansu mama,Su shayar da su.Amma mutanena sun zama kamar jiminai cikin jeji.
4 Harshen jinjiri ya liƙe a dasashinsa saboda ƙishi,'Yan yara suna roƙon abinci,Amma ba wanda ya ba su.