1 Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu.Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!
2 An ba baƙi gādonmu,Gidajenmu kuwa an ba bare.
3 Mun zama marayu, marasa ubanni,Uwayenmu sun zama kamar matan da mazajensu sun mutu.
4 Dole ne mu biya ruwan da za mu sha,Dole ne kuma mu sayi itace.
5 Masu binmu a ƙyeyarmu suke, suna korarmu da zafi,Mun gaji, ba a yarda mu huta.
6 Mun miƙa hannu ga Masar da AssuriyaDon mu sami abinci.