5 Masu binmu a ƙyeyarmu suke, suna korarmu da zafi,Mun gaji, ba a yarda mu huta.
6 Mun miƙa hannu ga Masar da AssuriyaDon mu sami abinci.
7 Ubanninmu sun yi zunubi, ga shi kuwa, ba su,Mu kuwa muna ɗaukar alhakin muguntarsu.
8 Bayi suke mulkinmu,Ba kuwa wanda zai cece mu daga hannunsu.
9 Sai mun yi kasai da ranmu kafin mu sami abinci,Domin akwai masu kisa a jeji.
10 Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu,Saboda tsananin yunwa.
11 An yi wa mata faɗe a cikin Sihiyona,Haka kuma aka yi wa budurwai a garuruwan Yahuza.