1 “Yanzu firistoci, ga umarni dominku.
2 Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
3 Ga shi, zan tsauta wa 'ya 'yanku, in watsa kāshin dabbobin hadayunku a fuskokinku, sa'an nan zan kore ku daga gabana.
4 Ta haka za ku sani ni na ba ku wannan umarni domin alkawarin da na yi wa Lawi ya tabbata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
5 “Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai.