3 Ga shi, zan tsauta wa 'ya 'yanku, in watsa kāshin dabbobin hadayunku a fuskokinku, sa'an nan zan kore ku daga gabana.
4 Ta haka za ku sani ni na ba ku wannan umarni domin alkawarin da na yi wa Lawi ya tabbata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
5 “Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai.
6 Koyarwar gaskiya tana cikin bakinsa, ba a sami kuskure a bakinsa ba. Ya yi tafiya tare da ni da salama da gaskiya. Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta.
7 Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.
8 “Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
9 Saboda haka, ni ma zan sa jama'ar Isra'ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa'ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”