8 “Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
9 Saboda haka, ni ma zan sa jama'ar Isra'ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa'ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”
10 Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu?
11 Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra'ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka.
12 Ubangiji zai lalatar da dukan wanda ya aikata wannan, wato wanda ya farka da wanda ya amsa, ko wanda yake kawo hadayu ga Ubangiji Mai Runduna.
13 Ga kuma abin da kuke yi. Kuna cika bagaden Ubangiji da hawaye, da kuka, da kururuwa domin ba zai ƙara karɓar hadayun da kuke kawo masa ba.
14 Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka.