1 Taku ta ƙare, ku masu shiryamugunta,Masu tsara mugunta a gadajensu!Sa'ad da gari ya waye, sai su aikatata,Domin ikon aikatawa yanahannunsu.
2 Sukan yi ƙyashin gonaki da gidaje,sai su ƙwace.Sukan zalunci mutum, su ƙwacegidansa da gādonsa.
3 Domin haka Ubangiji ya ce,Ga shi, yana shirya wa wannanjama'a masifa,Wadda ba za ku iya kuɓuta dagacikinta ba.Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba,Gama mugun lokaci ne.
4 A wannan rana za su yi karinmagana a kanku,Za su yi kuka da baƙin ciki maizafi,Su ce, “An lalatar da mu sarai!Ya sāke rabon mutanena,Ya kawar da shi daga gare ni!Ya ba da gonakinmu ga waɗandasuka ci mu da yaƙi.”
5 Don haka ba za ku sami wanda zai samuku ma'auniA taron jama'ar Ubangiji ba.