1 Jawabi a kan Nineba ke nan, a littafin wahayin Nahum na Elkosh.
2 Ubangiji Allah mai kishi ne, maisakayya,Ubangiji mai sakayya ne, maihasala.Ubangiji yakan ɗauki fansa a kanmaƙiyansa.Yana tanada wa maƙiyansa fushi.
3 Ubangiji mai jinkirin fushi ne,Mai Iko Dukka.Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifiba.Hanyarsa tana cikin guguwa da cikinhadiri,Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.
4 Yakan tsauta wa teku, sai teku taƙafe.Yakan busar da koguna duka.Bashan da Karmel sukan bushe,Tohon Lebanon yakan yanƙwane.
5 Duwatsu sukan girgiza a gabansa,Tuddai kuma su narke.Duniya ta murtsuke a gabansa,Da dukan mazauna a cikinta.
6 Wa zai iya tsaya wa fushinsa?Wa kuma zai iya daurewa dahasalarsa?Yana zuba hasalarsa mai kama dawuta,Duwatsu sukan farfasu a gabansa.