3 Ubangiji mai jinkirin fushi ne,Mai Iko Dukka.Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifiba.Hanyarsa tana cikin guguwa da cikinhadiri,Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.
4 Yakan tsauta wa teku, sai teku taƙafe.Yakan busar da koguna duka.Bashan da Karmel sukan bushe,Tohon Lebanon yakan yanƙwane.
5 Duwatsu sukan girgiza a gabansa,Tuddai kuma su narke.Duniya ta murtsuke a gabansa,Da dukan mazauna a cikinta.
6 Wa zai iya tsaya wa fushinsa?Wa kuma zai iya daurewa dahasalarsa?Yana zuba hasalarsa mai kama dawuta,Duwatsu sukan farfasu a gabansa.
7 Ubangiji mai alheri ne,Shi mafaka ne a ranar wahala.Ya san waɗanda suke fakewa a gareshi.
8 Zai shafe maƙiyansa da ambaliyarruwa,Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwacikin duhu.
9 Me kuke ƙullawa game da Ubangiji?Ubangiji zai wofintar da abin nan dakuke ƙullawa,Sau ɗaya kawai zai hallaka ku.