1 Wanda yake farfashewa ya aukomaka,Sai ka sa mutane a kagara, a yitsaron hanya,Ka yi ɗamara, ka tattaro ƙarfinkaduka.
2 Gama Ubangiji zai mayar waYakubu da darajarsa kamar taIsra'ila.Ko da masu washewa sun washe su,Sun kuma lalatar da rassan inabinsu.
3 Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne,Sojojinsa kuma suna saye da mulufi.Da ya shirya tafiya,Karusai suna walƙiya kamarharshen wuta,Ana kaɗa mashi da bantsoro.
4 Karusai sun zabura a tituna ahaukace.Suna kai da kawowa a dandali,Suna walwal kamar jiniya,Suna sheƙawa a guje kamarwalƙiya.
5 Sai aka kira shugabanni,Suka zo a guje suna tuntuɓe,Suka gaggauta zuwa garu,Suka kafa kagara.