3 Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne,Sojojinsa kuma suna saye da mulufi.Da ya shirya tafiya,Karusai suna walƙiya kamarharshen wuta,Ana kaɗa mashi da bantsoro.
4 Karusai sun zabura a tituna ahaukace.Suna kai da kawowa a dandali,Suna walwal kamar jiniya,Suna sheƙawa a guje kamarwalƙiya.
5 Sai aka kira shugabanni,Suka zo a guje suna tuntuɓe,Suka gaggauta zuwa garu,Suka kafa kagara.
6 An buɗe ƙofofin kogi,Fāda ta rikice.
7 An tsiraita sarauniya, an tafi da ita,'Yan matanta suna makoki, sunakuka kamar kurciyoyi,Suna bugun ƙirjinsu.
8 Nineba tana kama da tafki wandaruwansa yake zurarewa,Suna cewa, “Tsaya, tsaya,”Amma ba wanda ya waiga.
9 A washe azurfa!A washe zinariya!Dukiyar ba ta da adadi,Akwai dukiya ta kowane iri.