4 Karusai sun zabura a tituna ahaukace.Suna kai da kawowa a dandali,Suna walwal kamar jiniya,Suna sheƙawa a guje kamarwalƙiya.
5 Sai aka kira shugabanni,Suka zo a guje suna tuntuɓe,Suka gaggauta zuwa garu,Suka kafa kagara.
6 An buɗe ƙofofin kogi,Fāda ta rikice.
7 An tsiraita sarauniya, an tafi da ita,'Yan matanta suna makoki, sunakuka kamar kurciyoyi,Suna bugun ƙirjinsu.
8 Nineba tana kama da tafki wandaruwansa yake zurarewa,Suna cewa, “Tsaya, tsaya,”Amma ba wanda ya waiga.
9 A washe azurfa!A washe zinariya!Dukiyar ba ta da adadi,Akwai dukiya ta kowane iri.
10 Nineba ta halaka! ta lalace, ta zamakufai!Zukata sun narke, gwiwoyi sunakaɗuwa!Kwankwaso yana ciwo,Fuskoki duka sun kwantsare!