2 Ku ji amon bulala da kwaramniyarƙafafu,Da sukuwar doki da girgizar karusai!
3 Sojojin dawakai suna kai sura,Takuba suna walƙiya, māsu sunaƙyalƙyali.Ga ɗumbun kisassu, da tsibingawawwaki,Matattu ba su ƙidayuwa,Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!
4 Ya faru saboda yawan karuwancinNineba kyakkyawa mai daɗinbaki,Wadda ta ɓad da al'umman duniyada karuwancinta,Ta kuma ɓad da mutane da daɗinbakinta.
5 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Inagāba da ke,Zan kware fatarinki a idonki,Zan sa al'ummai da mulkoki su dubitsiraicinki.
6 Zan watsa miki ƙazanta,In yi miki wulakanci,In maishe ki abin raini.
7 Dukan waɗanda za su dube kiZa su ja da baya su ce,‘Nineba ta lalace, wa zai yi kukadominta?’A ina zan samo miki waɗanda za suta'azantar da ke?”
8 Kin fi No ne?Wadda take a bakin Nilu,Wadda ruwa ya kewaye ta?Teku ce kagararta.Ruwa ne kuma garunta.