3 Elimelek, mijin Na'omi, ya rasu, aka bar Na'omi da 'ya'yansu maza biyu.
4 Sai suka auri 'yan matan Mowab, Orfa da Rut. Bayan da suka yi wajen shekara goma a can,
5 sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.
6 Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.
7 Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.
8 Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.
9 Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su.Sai suka fashe da kuka,