10 Kitsonki yana da kyau a kumatunki,Ya sauka a wuyanki kamar lu'ulu'ai.
11 Mu kuma za mu ƙera miki sarƙar zinariya,A yi miki ado da azurfa.
12 A sa'ad da sarki yake kan kujerarsa,Yana jin daɗin ƙanshin turarena ƙwarai.
13 Ƙaunataccena yana da ƙanshin murLokacin da yake kwance a ƙirjina.
14 Ƙaunataccena kamar furen jeji yakeWanda yake huda a gonar inabi a En-gedi.
15 Ke kyakkyawa ce ƙwarai, kyakkyawa ce ke, ya ƙaunatacciyata,Idonki suna haskaka da ƙauna.
16 Kai kyakkyawa ne ƙwarai, ya ƙaunataccena, kana da bansha'awa.Koriyar ciyawa ita ce gadonmu.