2 Kamar yadda furen bi-rana yake a cikin ƙayayuwa,Haka ƙaunatacciyata take a cikin sauran mata.
3 Kamar yadda itacen gawasa yake a cikin itatuwan jeji,Haka ƙaunataccena yake a cikin sauran maza.Da farin ciki na zauna a inuwarsa,Ina jin daɗin halinsa ƙwarai.
4 Ya kai ni babban ɗakin da ake liyafa,Ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5 Ka ciyar da ni da wainar zabibi,Ka ba ni 'ya'yan gawasa in sha in wartsake!Gama na cika da sha'awarka.
6 Bari ka ta da kaina da hannun hagunka,Ka rungume ni da hannun damanka.
7 Ku 'yan matan Urushalima,Ku rantse da bareyi, da batsiyoyi,Ba za ku shiga tsakaninmu ba,Ku bar ta kurum.
8 Na ji muryar ƙaunataccena!Ya zo a guje daga kan tuddai,Ya sheƙo daga tuddai zuwa wurina.