7 Ku 'yan matan Urushalima,Ku rantse da bareyi, da batsiyoyi,Ba za ku shiga tsakaninmu ba,Ku bar ta kurum.
8 Na ji muryar ƙaunataccena!Ya zo a guje daga kan tuddai,Ya sheƙo daga tuddai zuwa wurina.
9 Ƙaunataccena kamar barewa yake,Kamar sagarin kishimi.Ga shi can, yana tsaye a bayan katangarmu.Yana leƙe ta tagogi,Yana kallona ta cikin asabari.
10 Ƙaunataccena ya yi magana da ni.Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa.
11 Gama lokacin sanyi ya wuce,Ruwa kuma ya ɗauke.
12 Furanni suna hudowa a itatuwa ko'ina.Lokacin raira Waƙoƙi ya yi,Lokacin da kurciyoyi suke kuka ya yi.
13 'Ya'yan ɓaure sun nuna,Tohon inabi yana ƙanshi.Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa!