6 Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ya riga ya tafi!Na so in ji muryarsa ƙwarai!Na neme shi, amma ban same shi ba.Na yi kiransa, amma ba amsa.
7 Matsara masu kai da kawowa cikin birni suka same ni,Suka doke ni suka yi mini rauni.Matsaran da suke kan garu suka fige gyalena.
8 Ku yi mini alkawari ku matan Urushalima,Idan kun ga ƙaunataccena,Ku faɗa masa na yi suwu saboda ƙauna.
9 Ke mafi kyau cikin mata,Ki faɗi yadda ƙaunatacce naki yake.Wane abin sha'awa take gare shi,Har da za mu yi miki alkawari?
10 Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma,Da ƙyar a sami ɗaya irinsa a cikin dubu goma.
11 Gashin kansa dogaye ne suna zarya,Baƙi wulik kamar jikin shaya.Kansa ya fi zinariya daraja.
12 Idanunsa kamar na kurciyoyi a bakin ƙorama,Waɗanda suka yi wanka da madara suna tsaye a bakin rafi.