1 Ke mafi kyau cikin matan,Ina ƙaunatacce naki ya tafi?Wace hanya ƙaunatacce naki ya bi?Za mu taimake ki nemansa.
2 Ƙaunataccena ya tafi lambunsa inda fangulan furanninsa suke.Yana kiwon garkensa a lambun, yana tattara furannin bi-rana.
3 Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce,Yana kiwon garkensa a cikin bi-rana.
4 Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima,Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza,Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.
5 Ki daina dubana gama idanunki suna rinjayata,Gashinki yana zarya kamar garken awakiDa yake gangarowa daga tuddan Gileyad.
6 Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausayaAka yi mata wanka nan da nan.Ba giɓi, suna nan shar.An jera su tantsai.
7 Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.