11 Sulemanu yana da gonar inabiA Ba'al-hamon, wato wuri mai yawan albarka.Ya yi ijara da waɗansu zaɓaɓɓun manoma.Kowannensu yana biyansa kuɗi, azurfa dubu.
12 Ni ma ina da gonar inabi ta kaina.Kai Sulemanu zan ba ka kuɗi azurfa dubu,Sauran ma'aikata kuma zan ba kowanne ɗari biyu.
13 Aminaina suna kasa kunne ga ƙaunataccena.Ina so in ji muryarka daga cikin lambun.
14 Ya ƙaunataccena, ka zo wurina da sauri, kamar batsiya,Ko sagarin kishimi a kan duwatsu inda kayan yaji yake tsirowa.