6 Rundunar ta aukar wa ƙasarmu,Tana da ƙarfi, ba ta kumaƙidayuwa,Haƙoranta suna da kaifi kamar nazaki.
7 Ta lalatar da kurangar inabinmu,Ta cinye itatuwan ɓaurenmu.Ta gaigaye ɓawo duka,Saboda haka rassan sun zama farifat.
8 Ya jama'a, ku yi kukaKamar yarinyar da take makokinrasuwar saurayinta.
9 Ba hatsi ko ruwan inabinDa za a yi hadaya da su cikinHaikalin.Firistoci masu miƙa wa Ubangijihadaya suna makoki.
10 Ba kome a gonaki,Ƙasa tana makoki,Domin an lalatar da hatsin,'Ya'yan inabi sun bushe,Itatuwan zaitun kuma sun yi yaushi.
11 Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki,Ku yi kuka, ku da kuke lura dagonakin inabi,Gama alkama, da sha'ir,Da dukan amfanin gonaki sunlalace.
12 Kurangar inabi ta bushe,Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi,Rumman, da dabino, da gawasa,Da dukan itatuwan gonaki sunbushe.Murna ta ƙare a wurin mutane.