2 Zan tattara dukan al'ummai,In kai su kwarin Yehoshafat.A can zan yi musu shari'aA kan dukan abin da suka yi wajama'ata.Sun warwatsa Isra'ilawa a sauranƙasashe,Suka rarraba ƙasata.
3 Sun jefa kuri'a a kan mutanena,Sun sayar da yara, mata da maza,zuwa bautaDon su biya karuwai da ruwaninabi.
4 “Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.
5 Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku.
6 Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa.
7 Yanzu zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, zan yi muku abin da kuka yi musu.
8 Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza 'ya'yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”