3 Ka jefa ni cikin zurfi,Can cikin tsakiyar teku,Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni,Kumfa da raƙuman ruwanka sukabi ta kaina.
4 Na ce, an kore ni daga wurinka,Duk da haka zan sāke ganinHaikalinka mai tsarki.
5 Ruwa ya sha kaina,Tekun ta rufe ni ɗungum.Tsire-tsiren teku suka naɗe kaina.
6 Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussanduwatsu.Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada,Amma ka fitar da ni daga cikinramin, ya Ubangiji Allahna.
7 Sa'ad da na ji raina yana rabuwa dani,Sai na tuna da kai, ya Ubangiji.Addu'ata kuwa ta kai gare ka aHaikalinka tsattsarka.
8 Su waɗanda suke yin sujada ga gumakamarasa amfaniSun daina yi maka biyayya.
9 Amma ni zan raira yabbai gare ka,Zan miƙa maka sadaka,Zan cika wa'adin da na yi.Ceto daga wurin Ubangiji yake.”