1 Ubangiji kuma ya sāke ce wa Yunusa,
2 “Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi musu shelar saƙon da zan faɗa maka.”
3 Sai Yunusa ya tashi ya tafi Nineba kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa. Nineba kuwa babban birni ne. Zai kai mutum tafiyar kwana uku kafin yă ƙure birnin.
4 Sai Yunusa ya kama tafiya yana ratsa birnin, da ya yi tafiyar yini guda, sai ya yi shela ya ce, “Nan da kwana arba'in za a hallaka Nineba.”