14 Mala'ikan kuma da yake magana da ni ya ce, in yi shela in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce yana jin ƙishin Urushalima da Sihiyona ƙwarai.
15 Yana fushi ƙwarai da al'umman duniya da take zaman lafiya, gama ya yi ɗan fushi da mutanena, amma su suka yi musu hukuncin da ya zarce.
16 Saboda haka shi Ubangiji zai koma ya ji juyayin Urushalima. Za a gina Haikalinsa a cikinta, zai kuma auna Urushalima da ma'auni.”
17 Ya ce, in kuma yi shela, in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce wadata za ta sake bunƙasa cikin biranensa, zai kuma ta'azantar da Sihiyona, ya kuma zaɓi Urushalima.”
18 Da na ɗaga idona, sai na ga ƙahoni huɗu.
19 Sai na ce wa mala'ikan da ya yi magana da ni, “Mene ne waɗannan?”Shi kuwa ya ce mini, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza, da Isra'ila, da Urushalima.”
20 Sa'an nan kuma Ubangiji ya nuna mini waɗansu maƙera, su huɗu.