1 Da na ɗaga idona, sai ga wani mutum yana riƙe da igiyar awo.
2 Sai na ce, “Ina za ka?”Ya ce mini, “Zan tafi in auna Urushalima don in san fāɗinta da tsawonta.”
3 Sai ga mala'ikan da yake magana da ni, ya fita, sai wani mala'ika kuma ya zo ya sadu da shi.
4 Ya ce masa, “Ka yi gudu, ka faɗa wa saurayin can, cewa za a zauna a Urushalima kamar a ƙauyuka marasa garu, saboda yawan mutane da dabbobi da suke cikinta.
5 Gama zan zama mata garu na wuta kewaye da ita, zan zama daraja a tsakiyarta, in ji Ubangiji.”
6 Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya!
7 Ya ke Sihiyona, ku tsere, ku waɗanda kuke zaune a Babila.”