6 Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya!
7 Ya ke Sihiyona, ku tsere, ku waɗanda kuke zaune a Babila.”
8 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona.
9 Ga shi, zan nuna ikona a kansu, za su kuwa zama abin waso ga waɗanda suka bauta musu. Sa'an nan za ku sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni.
10 “Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa.
11 “A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.
12 Yahuza za ta zama abin mallakar Ubangiji a cikin tsattsarkar ƙasar. Zai kuma zaɓi Urushalima.”