7 “Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Idan ka yi tafiya a hanyata, ka kuma kiyaye umarnina, zan sa ka zama shugaban Haikalina, ka lura da shirayina, zan kuma sa ka sami damar zuwa wurin waɗannan da yake tsaye.
8 Ka ji, ya Yoshuwa, babban firist, kai da abokanka da suke zaune gabanka, ku alama ce mai kyau. Ga shi, zan kawo bawana mai suna Reshe.
9 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a kan dutsen da na kafa a gaban Yoshuwa, dutse mai ido bakwai zan yi rubutu, zan kawar da laifin al'umman nan rana ɗaya.
10 A wannan rana kowane ɗayanku zai gayyaci maƙwabcinsa zuwa gindin kurangar inabinsa da itacen ɓaurensa.’ ”