1 Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama.
2 Sai mala'ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”
3 Sa'an nan ya ce mini, “Wannan la'ana ce wadda take tashi bisa ƙasa duka. Gama za ta datse ɓarawo da mai rantsuwa da ƙarya.
4 Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”
5 Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.”