2 Sai mala'ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”
3 Sa'an nan ya ce mini, “Wannan la'ana ce wadda take tashi bisa ƙasa duka. Gama za ta datse ɓarawo da mai rantsuwa da ƙarya.
4 Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”
5 Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.”
6 Ni kuwa na ce masa, “Mene ne wannan?”Ya ce, “Wannan babban kwando ne wanda ya fita.” Ya kuma ce, “Wannan mugunta ce a dukan ƙasar.”
7 Da aka ɗaga murfin kwando na darma, sai ga mace tana zaune a cikin kwandon!
8 Sai ya ce, “Wannan mugunta ce.” Sa'an nan ya tura ta cikin kwandon, ya rufe bakin kwandon da murfi na darma mai nauyi.