7 Da aka ɗaga murfin kwando na darma, sai ga mace tana zaune a cikin kwandon!
8 Sai ya ce, “Wannan mugunta ce.” Sa'an nan ya tura ta cikin kwandon, ya rufe bakin kwandon da murfi na darma mai nauyi.
9 Da na ɗaga idona, sai na ga mata biyu suna matsowa. Iska tana hura fikafikansu, gama suna da fikafikai kamar na shamuwa. Suka ɗaga kwandon sama.
10 Sai na tambayi mala'ikan da yake magana da ni, na ce, “Ina za su kai kwandon?”
11 Ya ce mini, “Za su tafi da shi ƙasar Shinar don su gina masa haikali, sa'ad da suka gama ginin, za su ajiye shi a ciki.”