18 Ubangiji Mai Runduna ya yi magana da ni, ya ce,
19 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama'ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.
20 “Mutanen birane da yawa za su hallara.
21 Mutanen wani birni za su tafi wurin mutanen wani birni, su ce musu, ‘Za mu tafi mu roƙi alherin Ubangiji, mu kuma nemi Ubangiji Mai Runduna. Ku zo mu tafi.’
22 Jama'a da yawa da al'ummai masu iko za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Mai Runduna, su kuma roƙi alherin Ubangiji.
23 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al'umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ”