3 Zan koma wurin Sihiyona, in zauna a tsakiyar Urushalima. Za a ce da Urushalima birnin gaskiya, da kuma dutsen Ubangiji Mai Runduna, tsattsarkan dutse.
4 Tsofaffi, mata, da maza, za su zauna a titunan Urushalima, kowa yana tokare da sanda saboda tsufa.
5 Samari da 'yan mata zan sa su cika titunan Urushalima, suna wasa.
6 “Idan abin nan ya zama mawuyaci ga sauran jama'a a kwanakin nan, zai zama mawuyacin abu ne a gare ni?
7 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, zan ceci mutanena daga ƙasar gabas da ƙasar yamma.
8 Zan kawo su su zauna a Urushalima. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu da gaskiya da adalci.
9 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.