1 Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,
2 don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku.
3 Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa,
4 sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali'u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.
5 Don dā ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu,
6 kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma 'ya'yanta ne muddin kuna aiki nagari, ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.