15 kada wani ya ce da sunana ne aka yi muku baftisma.
16 Ai, kuwa lalle na yi wa jama'ar gidan Istifanas ma. Amma banda waɗannan ban san ko na yi wa wani baftisma ba.
17 Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.
18 Maganar gicciye, maganar wauta ce ga waɗanda suke hallaka, amma ƙarfin Allah ce a gare mu, mu da ake ceto.
19 Domin a rubuce yake cewa,“Zan rushe hikimar mai hikima,Zan kuma shafe haziƙancin haziƙi.”
20 To, ina masu hikima suke? Ina kuma masana? Ina masu muhawwarar zamanin nan? Ashe, Allah bai fallashi hikimar duniyar nan a kan wauta ce ba?
21 Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara.