1 To, ina so ku sani, 'yan'uwa, dukan kakanninmu an kāre su ne a ƙarƙashin gajimare, dukansu kuma sun ratsa ta cikin bahar.
2 Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin.
3 Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu,
4 duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.
5 Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.