14 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka.
15 Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.
16 Ƙoƙon nan na yin godiya, wanda muke gode wa Allah saboda shi, ashe, ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Gurasar nan da muke gutsuttsurawa kuma, ashe, ba tarayya ce ga jikin Almasihu ba?
17 Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci.
18 Ku dubi ɗabi'ar Isra'ila. Ashe, waɗanda suke ci daga hadayu, ba tarayya suke yi da bagadin hadaya ba?
19 Me nake nufi ke nan? Abin da aka yanka wa gumakan ne ainihin wani abu, ko kuwa gunkin ne ainihin wani abu?
20 A'a! Na nuna ne kawai cewa abin da al'ummai suke yankawa, ga aljannu suke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu.