14 Ashe, ko ɗabi'a ma ba ta nuna muku cewa namiji ya yi gizo, abin kunya ne ba?
15 In kuwa mace tana da gashi, ba alfarmarta ce ba? Gama don rufin kai ne aka yi mata gashin.
16 In kuwa wani yana da niyyar gardama, to, mu dai ba mu san wata al'ada ba, ikilisiyoyin Allah kuma haka.
17 A game da umarnin nan kuwa, ban yaba muku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin kirki ce.
18 To, da farko dai sa'ad da kuka taru, taron ikkilisiya, na ji har akwai rarrabuwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.
19 Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.
20 Ashe kuwa, in kun taru gu ɗaya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!