5 Amma duk matar da ta yi addu'a, ko ta yi annabci da kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta ke nan, duk ɗaya ne da an aske kanta ma.
6 In mace ta ƙi rufe kanta, to, sai ta sausaye gashinta. In kuwa abin kunya ne a yi wa mace sausaye ko kundumi, to, sai ta rufe kanta.
7 Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.
8 (Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba, amma matar daga jikin namiji take.
9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.)
10 Shi ya sa ya kamata mace ta rufe kanta, wato, alamar ikon namiji, saboda mala'iku.
11 Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.