32 Annabawa suna sarrafa ruhohinsu na annabci,
33 domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne.Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka.
34 Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce.
35 In akwai wani abin da suke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin taron ikkilisiya.
36 A kanku ne maganar Allah ta fara, ko kuwa a gare ku kaɗai ta isa?
37 In wani yana zato shi annabi ne, ko kuwa mai wata baiwa ta ruhu, to, sai yă fahimta, abin nan da nake rubuto muku umarni ne na Ubangiji.
38 In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.